23 Afirilu 2022 - 18:36
An Kashe Sojojin Kasar Pakistan 3 A Wani Wuri Dake Iyakarta Da Kasar Afghanistan

Majiyar soji ta kasar Pakistan ta bayyana cewa sojojin kasar Pakistan guda 3 ne aka kashe a iyakar ta da Kasar Afghanistan a lardin Khyber a wani hari da aka kai musu daga kasar Afghanistan A yau Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bayanin ya ci gaba da cewa wasu yan ta’adda ne daga kasar Afghanistan suka ketara iyakar kasa da kasa kana suka bude wuta kan dakarun tsaron iyaka na kasar Pakistan a Arewacin Waziristan , sai dai jami’an tsaron sun mayar da martani a nan take kana sun jawo mummunar asarar rayukan ga yan ta’addan.

Khyber Pakhtunkwa yana daga cikin larduna da suke da matsalar tsaro a kasar ta Pakistan inda ya zuwa yanzu an kashe jami’n soji da fararen hula da dama a yankin sakamakon hare-haren da yan ta’adda suke kai wa.

Kungiyar Taliban Pakistan da aka fi sani da Tahrikh e Taliban Pakistan sun raba gari da ainihin kungiyar Taliban da ta karbe gwamnati a kasar Afghanistan a watan Agusta na shekarar da ta gabata, tun daga nan take ci gaba da kai hare-hare kan jami’an tsaro a yankin da ma wasu yankunan daban.

342/